Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Publicans: Disreputable

7 ayoyi · 19 fannoni

Ayoyi game da Disreputable

  1. In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?

  2. In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba?

  3. Sa’ad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da masu zunubi?”

  4. Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”

  5. In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.

  6. “Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.

  7. Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan.