Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Profane Swearing

23 ayoyi · 11 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.

  2. Ɗan mutuniyar Isra’ila ya saɓi Sunan Ubangiji, ya kuma la’ana shi, saboda haka aka kawo shi wa Musa. (Sunan mahaifiyarsa Shelomit ne, ’yar Dibri na kabilar Dan.)

  3. duk wanda ya saɓi sunan Ubangiji, dole a kashe shi. Dole jama’a gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Ko baƙo, ko haifaffen ɗan ƙasa, sa’ad da ya saɓi Sunan Ubangiji, dole a kashe shi.

  4. Sai Musa ya yi wa Isra’ilawa magana, suka kuwa kai mai saɓon waje da sansani, suka jajjefi shi da duwatsu. Isra’ilawa suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  5. Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai ba wa duk mai yin amfani da sunansa a banza laifi.

  6. sai Gehazi, bawan Elisha mutumin Allah, ya yi tunani a ransa ya ce, “Maigidana ya yi wa Na’aman mutumin Aram nan ƙaramci da bai karɓi duk abin da ya kawo ba. Muddin Ubangiji yana a raye, zan bi shi a guje in karɓi wani abu daga gare shi.”

  7. Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana; wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.

  8. Saboda zunuban bakunansu, saboda maganganun leɓunansu, bari a kama su cikin fariyarsu. Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,

  9. Yana jin daɗin la’antarwa, bari yă dawo a kansa; ba ya son sa albarka, bari kada kowa yă sa masa albarka.

  10. Ya sa la’antarwa kamar rigarsa; ta shiga cikin jikinsa kamar ruwa, cikin ƙasusuwansa kamar mai.

  11. Ƙasar ta cika da mazinata; saboda la’ana ƙasar ta zama kango makiyaya a hamada ta bushe. Annabawa suna bin mugayen muradu suna kuma amfani da ƙarfinsu a hanyar marar kyau.

  12. Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa, gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar. “Babu aminci, babu ƙauna, babu yarda da Allah a cikin ƙasar.

  13. Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa, yin sata da zina; sun wuce gona da iri, kisankai a kan kisankai.

  14. Saboda wannan ƙasar tana makoki, kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace; namun jeji da tsuntsayen sararin sama da kuma kifin teku suna mutuwa.

  15. Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne;

  16. ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne.

  17. Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba.

  18. “Kaitonku, makafi jagora! Kukan ce, ‘In wani ya rantse da haikali, ba damuwa; amma in ya rantse da zinariyar haikali, sai rantsuwar ta kama shi.’

  19. Kuma duk wanda ya rantse da haikali, ya rantse ne da shi da kuma wanda yake zaune a cikinsa.

  20. Duk kuma wanda ya rantse da sama, ya rantse ne da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune a kansa.

  21. Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!” Nan da take, sai zakara ya yi cara.

  22. “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”

  23. ’Yan’uwana, fiye da kome, kada ku yi rantsuwa ko da sama, ko da ƙasa ko da wani abu dabam. Bari “I” naku yă zama “I”. “A’a” naku kuma yă zama “A’a”, don kada a hukunta ku.