Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pontius Pilate: Allows Joseph of Arimathaea to take Jesus' body

7 ayoyi · 4 fannoni

Ayoyi game da Allows Joseph of Arimathaea to take Jesus' body

  1. Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne.

  2. Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yă ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi.

  3. Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

  4. Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu.

  5. Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin.

  6. Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

  7. Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin.