Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Peter: Confesses Jesus as Christ

8 ayoyi · 35 fannoni

Ayoyi game da Confesses Jesus as Christ

  1. Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai.”

  2. Yesu ya amsa ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama.

  3. Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus,a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hadesba za su rinjaye ta ba.

  4. Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”

  5. Sai ya yi tambaya ya ce, “Amma ku fa, wa kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi.”

  6. “Amma ku fa, wa, kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kiristi na Allah.”

  7. Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami.

  8. Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”