Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Panic: From God

15 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da From God

  1. Sa’an nan suka kama hanya, tsoron Allah kuwa ya kama dukan garuruwan da suke kewayensu har babu wanda ya iya bin su.

  2. Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki tsoro zai kama mutanen Filistiya.

  3. Sarakunan Edom za su tsorata, shugabannin Mowab za su yi rawar jiki, mutanen Kan’ana za su narke.

  4. Razana da tsoro za su fāɗo a kansu. Da ikon hannunka za su tsaya cik kamar dutse, har sai mutanen da ka kawo sun wuce, ya Ubangiji.

  5. Sa’ad da aka busa ƙahonin nan ɗari uku sai Ubangiji ya sa Midiyawa suka yi ta saran juna. Mayaƙan suka gudu zuwa Bet-Shitta wajen Zerera har zuwa yankin Abel-Mehola kusa da Tabbat.

  6. Sai tsoro ya kama dukan sojojin Filistiyawa, waɗanda suke cikin sansanin da waɗanda suke fili, har da waɗanda suke waje, da kuma waɗanda suke kai hari, ƙasa ta girgiza. Allah ne ya kawo wannan rikicewa.

  7. Masu gadin Shawulu a Gebiya da take a Benyamin suka duba sai ga rundunar Filistiyawa a warwatsewa ko’ina.

  8. Sai Shawulu ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ku ƙidaya mayaƙa ku ga wane ne ba ya nan.” Da suka ƙirga sai suka tarar Yonatan da mai ɗaukan makamansa ba sa nan.

  9. Shawulu ya ce wa Ahiya, “Kawo akwatin alkawarin Allah.” (A lokacin akwatin alkawarin yana tare da Isra’ilawa.)

  10. Yayinda Shawulu yake magana da firist kuwa, harguwa ya yi ta ƙaruwa a sansanin Filistiyawa. Sai Shawulu ya ce wa firist, “Janye hannunka.”

  11. Sa’an nan Shawulu da dukan mutanensa suka taru suka tafi yaƙi. Suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna yaƙi da juna da takubansu.

  12. gama Ubangiji ya sa rundunar Arameyawa suka ji motsin kekunan yaƙi, da motsin dawakai, da na babban rundunar sojoji, saboda haka suka ce wa juna; “Duba, sarkin Isra’ila ya ɗauka hayar sarakuna Hittiyawa da sarakunan Masarawa don su yaƙe mu!”

  13. Saboda haka suka tashi, suka gudu da yamma, suka bar tentunansu, da dawakansu, da jakunansu. Suka bar sansanin yadda yake, suka gudu don su ceci rayukansu.

  14. Da suka fara waƙa, suna kuma yabo, sai Ubangiji ya kai hari a kan mutanen Ammon da Mowab da Dutsen Seyir, waɗanda suka kawo hari a Yahuda, aka kuwa ci su da yaƙi.

  15. Mutanen Ammon da Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa’ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka juna.