Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Night: Divided into watches

9 ayoyi · 42 fannoni

Ayoyi game da Divided into watches

  1. Da asubahin fāri, sai Ubangiji ya dubi ƙasa a kan sojojin Masarawa daga al’amudin wuta da kuma girgije, sai ya sa suka ruɗe.

  2. Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu.

  3. Gari yana wayewa, sai Shawulu ya raba mutane kashi uku, a sa’a ta ƙarshe na daren sai suka fāɗa wa sansanin Ammonawa, suka kuma karkashe su har lokacin da rana ta yi zafi. Waɗanda suka kuɓuce kuwa suka warwatsu, har babu biyunsu da aka bari tare.

  4. Bakbukiya da Unni, ’yan’uwansu sun tsaya ɗaura da su a hidimomi.

  5. A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.

  6. Ban rufe idanuna ba dukan dare, don in yi tunani a kan alkawuranka.

  7. Ki tashi, ki yi kuka cikin dare, dare na yi sai ki fara kuka; kina buɗewa Ubangiji zuciyarki. Ki ɗaga hannuwanki gare shi domin rayukan ’ya’yanki, waɗanda suka suma don yunwa a kan kowane titi.

  8. Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.

  9. Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a sa’a ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne.