Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Net

36 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Aka yi yanar tuƙaƙƙun sarƙoƙi aka ɗaura dajiyoyin a bisa ginshiƙai guda bakwai don kowace dajiya.

  2. Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga, yana ta yawo a cikin ragar.

  3. sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba ya kewaye ni da ragarsa.

  4. Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu; aka kama ƙafafunsu a ragar da suka ɓoye.

  5. Yakan yi kwanto a ɓoye kamar zaki. Yakan yi kwanto don yă kama marasa ƙarfi; yakan kama marasa ƙarfi yă ja su cikin ragarsa.

  6. Idanuna kullum suna a kan Ubangiji, gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.

  7. Ka ’yantar da ni daga tarkon da aka sa mini, gama kai ne mafakata.

  8. Da yake sun ɓoye tarko domina ba dalili kuma babu dalili suka haƙa mini rami,

  9. bari lalaci yă kama su ba zato, bari tarkon da suka ɓoye yă kama su, bari su fāɗa cikin ramin, yă kai ga lalacinsu.

  10. Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna, damuwa ta sha ƙarfina. Sun haƙa rami a hanyata, amma su kansu suka fāɗa a cikinta. Sela

  11. Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu.

  12. Masu girman kai sun sa mini tarko; sun shimfiɗa igiyoyin ragarsu sun kuma shirya mini tarko a hanyata. Sela

  13. Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu, amma bari ni in zo in wuce lafiya.

  14. Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye!

  15. Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane, amma saiwar masu adalci kan haɓaka.

  16. Duk wanda yake wa maƙwabcinsa daɗin baki yana sa wa ƙafafunsa tarko ne.

  17. Sai na iske wani abin da ya fi mutuwa ɗaci mace wadda take tarko ne, wadda zuciyarta tarko ne wadda kuma hannuwanta sarƙa ne. Mutumin da ya gamshi Allah zai tsere mata, amma za tă kama mai zunubi.

  18. Ban da haka ma, ba wanda ya san sa’ad da lokacin mutuwarsa zai yi. Kamar yadda akan kama kifi a muguwar raga, ko a kama tsuntsu a tarko, haka mugun lokaci yakan auko wa mutane, ba tsammani.

  19. Masu kamun kifi za su yi nishi su kuma yi makoki, dukan waɗanda suke jefan ƙugiyoyi a Nilu; waɗanda suke jefan abin kamun kifi a ruwa abin kamun kifin za su zama marasa amfani.

  20. ’Ya’yanki sun sume; sun kwanta kusurwar kowane titi, kamar barewar da aka kama da tarko. Sun cika da fushin Ubangiji da kuma tsawatawar Allahnki.

  21. Za tă zama wurin shanya abin kamun kifi a tsakiyar teku, gama na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Za tă zama ganima ga sauran al’ummai,

  22. Zan maishe ki fā, za ki kuma zama wurin shanya abin kamun kifi. Ba za a sāke gina ki ba, gama Ni Ubangiji na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  23. Masunta za su tsaya a gaɓar; daga En Gedi zuwa En Eglayim, za a kasance da wuraren jefa abin kamun kifi. Za a sami kifayen iri-iri, kamar kifaye Bahar Rum.

  24. Sa’ad da suka tafi, zan jefa ragata a kansu; zai janye su ƙasa kamar tsuntsayen sararin sama. Sa’ad da na ji suna tafiya tare, zan kama su.

  25. Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne.