Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Meat Offerings

49 ayoyi · 28 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha.

  2. Ka miƙa ɗaya ragon da yamma, tare da hadaya ta gari da hadaya ta sha kamar aka yi ta safe, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  3. “Wannan za tă zama hadaya ta ƙonawar da za a dinga yi kowace rana, daga tsara zuwa tsara. Za a yi ta miƙa hadayar a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. A can zan sadu da kai, in yi magana da kai;

  4. Ba za a ƙona wani irin turare dabam a bisa wannan bagade ba, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta hatsi, ko ta sha a bisansa ba.

  5. Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  6. “ ‘Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, hadayarsa za tă zama gari mai laushi ne. Zai zuba mai a kai, yă sa turare a kansa

  7. yă kai wa ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci. Firist zai ɗiba gari mai laushin a tafin hannu da kuma man, tare da dukan turaren, yă ƙone wannan a sashen tunawa a kan bagade, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

  8. Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta.

  9. “ ‘In kuka kawo toyayyen hadayar gari da aka yi daga matoya, zai ƙunshi gari mai laushi, toyayye ba tare da yisti ba, gauraye kuma da mai, ko kuwa ƙosai da aka yi ba tare da yisti ba, aka kuma kwaɓa da mai.

  10. In an toya hadaya ta garinku a kasko, sai a yi shi da gari mai laushi haɗe da mai, ba kuwa da yisti ba.

  11. In hadayarku ta hatsin da aka dafa ne a tukunya, sai a yi shi da gari mai laushi da kuma mai.

  12. Zai fid da sashen tunawa daga hadaya ta gari, yă ƙone shi a kan bagade kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

  13. “ ‘Kowace hadaya ta garin da kuka kawo ga Ubangiji, dole a yi shi ba tare da yisti ba, gama ba za ku ƙone wani yisti, ko zuma a cikin hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta ba.

  14. A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku.

  15. “ ‘In kuka kawo hadaya ta gari na ’ya’yan fari ga Ubangiji, sai ku miƙa ɓarzajjen kawunan sabon hatsin da aka gasa a wuta.

  16. A sa mai da turare a kansa, hadaya ce ta hatsi.

  17. Firist zai ƙone sashe na ɓarzajjen hatsin da kuma mai, tare da turare don tunawa, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  18. “ ‘In ba zai iya kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ba, sai yă kawo humushin garwan gari mai laushi domin hadaya don zunubi. Ba lalle ba ne yă sa mai ko turare a kansa, saboda wannan hadaya ce ta zunubi.

  19. Firist zai ɗiba garin hadayar mai laushin wanda aka zuba masa mai da kuma turare cike da tafin hannu. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa.

  20. Haruna da ’ya’yansa maza za su ci sauran, amma za a ci shi ba tare da yisti ba a tsattsarkan wuri; za su ci shi a harabar Tentin Sujada.

  21. Ba za a toya shi da yisti ba; na ba su yă zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi.

  22. Kowane ɗa namiji cikin zuriyar Haruna zai iya cinsa. Wannan rabonsa ne na kullum na hadayar da aka yi ga Ubangiji da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk abin da ya taɓa hadayun zai tsarkaka.’ ”

  23. “Wannan ne hadayar da Haruna da ’ya’yansa maza za su kawo ga Ubangiji a ranar da za a naɗa su firistoci, humushin garwan gari mai laushi a matsayin hadaya ta gari na kullum, rabinsa da safe, rabinsa kuma da yamma.

  24. A shirya shi da mai a kwanon tuya, a kawo shi kwaɓaɓɓe sosai, a miƙa shi hadaya ta gari dunƙule-dunƙule don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

  25. Duk wanda aka naɗa daga ’ya’yan Haruna yă zama firist a madadinsa, shi ne zai miƙa wannan hadayar ga Ubangiji. Zai ƙone hadayar ƙurmus. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce har abada.