Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Maachah: 4. Called Michaiah, mother of Abijam and grandmother of Asa

8 ayoyi · 10 fannoni

Ayoyi game da 4. Called Michaiah, mother of Abijam and grandmother of Asa

  1. ya yi mulki a Urushalima shekara arba’in da ɗaya. Sunan mahaifiya mahaifiyarsa, Ma’aka ne ’yar Abisalom.

  2. Asa ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi.

  3. Ya kori dukan maza karuwai na masujadai daga ƙasar, ya kuma yi waje da dukan gumakan da mahaifinsa ya yi.

  4. Ya tuɓe mahaifiya mahaifiyarsa Ma’aka daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, gama ta gina ƙazantaccen ginshiƙin Ashera. Asa ya yanke ginshiƙin, ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron.

  5. Sa’an nan ya auri Ma’aka ’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit.

  6. Rehobowam ya ƙaunaci Ma’aka ’yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwarƙwaransa. Duka-duka dai ya auri mata goma sha takwas da ƙwarƙwarai sittin, yana da ’ya’ya maza ashirin da takwas da ’ya’ya mata sittin.

  7. Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma’aka yă zama babba yerima a cikin ’yan’uwansa, don dai yă naɗa shi sarki.

  8. Ya yi hikima, ya watsar da waɗansu ’ya’yansa a dukan yankunan Yahuda da Benyamin, da kuma a dukan birane masu katanga. Ya ba su tanadi mai yawa ya kuma aurar musu mata masu yawa.