Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Industry: General references

39 ayoyi · 23 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.

  2. Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.

  3. Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka;

  4. domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.

  5. Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai,

  6. gashin raguna za su tanada maka tufafi, za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki.

  7. Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata.

  8. Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani;

  9. remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu;

  10. fāra ba su da sarki, duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma;

  11. ana iya kama ƙadangare da hannu, duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna.

  12. Takan zaɓi ulu da lilin ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.

  13. Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa.

  14. Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.

  15. Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.

  16. Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.

  17. Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.

  18. Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.

  19. Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata.

  20. Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri.

  21. Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa; tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.

  22. Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni inda yakan zauna a cikin dattawan gari.

  23. Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.

  24. Ƙarfi da mutunci su ne suturarta; za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.

  25. Tana magana da hikima, kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.