Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Hushai

10 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Da Dawuda ya isa ƙwanƙoli, inda mutane sun saba yi wa Allah sujada, Hushai, mutumin Arkitawa kuwa yana can don yă tarye shi, taguwarsa a yage, ga kuma ƙura a kansa.

  2. Sai Dawuda ya ce masa, “In ka tafi tare da ni, za ka zama mini kaya.

  3. Amma in ka koma birni, ka gaya wa Absalom, ‘Zan zama bawanka, ya sarki; dā ni bawan mahaifinka ne, amma yanzu zan zama bawanka,’ ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel.

  4. Ba Zadok da Abiyatar firistocin nan suna nan tare da kai ba? Ka gaya musu duk abin da ka ji a fadan sarki.

  5. ’Ya’yansu biyu maza, Ahimawaz ɗan Zadok, da kuma Yonatan ɗan Abiyatar, suna can tare da su. Ka aike su wurina da duk abin da ka ji.”

  6. Saboda haka Hushai abokin Dawuda ya isa Urushalima yayinda Absalom yake shigowa birnin.

  7. Sai Hushai mutumin Arkitawa, abokin Dawuda ya je wurin Absalom ya ce masa, “Ran sarki yă daɗe! Ran sarki yă daɗe!”

  8. Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake nuna wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”

  9. Hushai ya ce wa Absalom, “A’a, ai, wanda Ubangiji ya zaɓa ta wurin waɗannan mutane, da kuma ta wurin dukan mutane Isra’ila, shi zan zama nasa, zan kuma kasance tare da shi.

  10. Ban da haka ma, wane ne zan bauta wa? Ashe, ba ɗan ne zan bauta wa ba? Kamar dai yadda na bauta wa mahaifinka, haka zan bauta maka.”