Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Government

62 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, akwai ’ya’ya maza saba’in na gidan Ahab a Samariya. Saboda haka Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika su Samariya, zuwa ga shugabannin Yezireyel, da kuma ga masu lura da ’ya’yan Ahab. Ya ce,

  2. “Da zarar wasiƙan nan ta sadu da ku, da yake ’ya’yan maigidanku suna tare da ku, kuna kuma da kekunan yaƙi da dawakai, da birni mai katanga da makamai,

  3. sai ku zaɓi mafi cancanta a cikin ’ya’yan maigidanku ku sa shi a kan kursiyin mahaifinsa. Sa’an nan ku yi yaƙi don gidan maigidanku.”

  4. Amma suka razana suka ce, “Idan sarakuna biyu ba su iya yin tsayayya da shi ba, wane mu?”

  5. Saboda haka sarkin fada, da gwamnan birnin, da dattawa, da kuma masu lura da ’ya’yan suka aika da saƙo ga Yehu, cewa, “Mu bayinka ne, za mu kuma yi duk abin da ka ce. Ba za mu naɗa kowa sarki ba; sai ka yi abin da ka ga ya fi kyau.”

  6. Sai Yehu ya sāke rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “In a gefena kuke, to, sai ku yi biyayya da ni, ku fille kawunan ’ya’yan maigidanku, ku kawo mini a Yezireyel war haka gobe.” To, ’ya’yan sarki, su saba’in, suna tare da manyan birni waɗanda suke lura da su.

  7. Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan ’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel.

  8. Biye da shi, ’yan’uwansu Lawiyawa ne a ƙarƙashin Binnuyi ɗan Henadad, mai mulkin ɗayan rabin yankin Keyila suka yi gyare-gyaren.

  9. Biye da su, Ezer ɗan Yeshuwa, mai mulkin Mizfa, ya yi gyara wani sashe, daga inda yake fuskantar hawan gidan makamai har zuwa kusurwa.

  10. Ya gamshi Dariyus ya naɗa muƙaddasai 120 su yi shugabanci a duk fāɗin masarautar,

  11. ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome.

  12. To, Daniyel dai ya yi ficce a cikin shugabannin nan uku har da muƙaddasan ma, saboda waɗansu halaye nagari da yake da su, wanda ya sa sarki ya yi shiri ya ɗora shi a kan dukan mulkinsa.