Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Formalism

56 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ba na tsawata muku saboda hadayunku ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana.

  2. Ba na bukatan bijimi daga turkenku ko awaki daga garkunanku,

  3. gama kowace dabbar kurmi nawa ne, da kuma shanu a kan dubban tuddai.

  4. Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu kuma halittun filaye nawa ne.

  5. Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta.

  6. Ina cin naman bijimai ne ko ina shan jinin awaki ne?

  7. “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,

  8. ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”

  9. Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo; ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.

  10. Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.

  11. Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.

  12. Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.

  13. Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku, mene ne suke a gare ni?” Ina da isashen hadayun ƙonawa, na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba; ba na jin daɗin jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki.

  14. Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana, wa ya nemi wannan daga gare ku, da kuke kai da kawowa a filayen gidana?

  15. Ku daina kawo hadayu marasa amfani! Turarenku abin ƙyama ne gare ni. Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini, ba zan iya jure wa mugun taronku ba.

  16. Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku na ƙi su. Sun zama mini kaya; na gaji da ɗaukansu.

  17. Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini!

  18. Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu suka kuma girmama ni da leɓunansu, amma zukatansu suna nesa daga gare ni. Sujadar da suke mini cike take da dokokin da mutane suka koyar.

  19. Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya da abubuwan banmamaki a kan abubuwan banmamaki; hikimar masu hikima za tă lalace, azancin masu azanci zai ɓace.”

  20. Kaiton waɗanda suke zuwa manyan zurfafa don su ɓoye shirye-shiryensu daga Ubangiji, waɗanda suke aikinsu cikin duhu su yi tunani, “Wa yake ganinmu? Wa zai sani?”

  21. Kuna birkitar abubuwa, sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu! Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi, “Ba shi ne ya yi ni ba”? Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane, “Ba ka san kome ba”?

  22. “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini; ba na son ganin tarurrukanku.

  23. Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi, ba zan karɓa ba. Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta, ba zan ɗauke su a bakin kome ba.

  24. Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku! Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.

  25. Da me zan zo a gaban Ubangiji in rusuna a gaban Maɗaukaki Allah? Shin, zan zo ne a gabansa da hadaya ta ƙonawa, da ɗan maraƙi bana ɗaya?