Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Confederacies

12 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A zamanin Amrafel sarkin Shinar, shi da Ariyok sarkin Ellasar, Kedorlayomer sarkin Elam, da kuma Tidal sarkin Goyim

  2. suka tafi don su yaƙi Bera sarkin Sodom, Birsha sarkin Gomorra, Shinab sarkin Adma, Shemeber sarkin Zeboyim, da kuma sarkin Bela (wato, Zowar).

  3. Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya ji cewa Yoshuwa ya ci Ai da yaƙi ya kuma hallaka ta sarai, ya yi wa Ai da sarkinta abin da ya yi wa Yeriko da sarkinta, mutanen Gibeyon kuwa sun yi yarjejjeniya ta salama da Isra’ilawa, suna kuma zama kusa da su.

  4. Shi da mutanensa suka ji tsoron wannan sosai, gama Gibeyon muhimmiyar birni ce, har ma kamar ɗaya daga cikin biranen sarauta, ya ma fi Ai girma, mazanta duka kuwa mayaƙa ne na ƙwarai.

  5. Saboda haka sai Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya roƙi Hoham sarkin Hebron, Firam sarkin Yarmut, Yafiya sarkin Lakish da Debir sarki Eglon ya ce,

  6. “Ku zo ku taimake ni in kai wa Gibeyon hari. Domin sun yi yarjejjeniya ta salama da Yoshuwa da Isra’ilawa.”

  7. Sai sarakunan nan biyar na Amoriyawa, sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon suka haɗa sojojinsu. Suka je dukansu suka yi shirin kai wa Gibeyon hari.

  8. Sa’ad da Yabin sarkin Hazor ya ji wannan, sai ya aika saƙo zuwa wurin Yobab sarkin Madon, da sarkin Shimron, da Akshaf,

  9. ya kuma aika zuwa ga sarakunan arewa waɗanda suke kan tuddai da kuma waɗanda suke cikin Araba a kudancin Kinneret da cikin filayen kwari, da cikin Nafot Dor a yamma;

  10. ya kuma aika zuwa ga Kan’aniyawa a gabas da yamma; da kuma zuwa ga Amoriyawa, Hittiyawa da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke kan tuddai; da kuma Hiwiyawa masu zama a gindin dutsen Hermon a yankin Mizfa.

  11. Suka fito da dukan rundunansu da keken yaƙi masu yawan gaske, babbar runduna, yawansu ya yi kamar yashin bakin teku.

  12. Duk sarakunan nan suka haɗa mayaƙansu tare, suka kafa sansani a bakin Ruwayen Meron don su yi yaƙi da Isra’ilawa.