Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Boasting

66 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci,

  2. gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah,

  3. an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi.

  4. Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba

  5. ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.

  6. To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙa’ida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? A’a, sai dai ta wurin bangaskiya.

  7. Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba.

  8. Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Al’ummai ba ne? I, shi Allahn Al’ummai ne ma,

  9. da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin.

  10. To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi.

  11. In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,

  12. kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi la’akari da wannan. Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka.

  13. To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.”

  14. Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro.

  15. Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.

  16. Gama Kiristi bai aike ni yin baftisma ba, sai dai wa’azin bishara ba da kalmomin hikimar mutum ba, domin kada gicciyen Kiristi ya rasa ikonsa.

  17. Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne.

  18. Gama a rubuce yake cewa, “Zan rushe hikimar mai hikima, basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”

  19. Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba?

  20. Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara.

  21. Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima,

  22. amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai,

  23. amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah.

  24. Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.

  25. ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa.