Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Amorites: Not exterminated

12 ayoyi · 10 fannoni

Ayoyi game da Not exterminated

  1. Amoriyawa suka matsa wa mutanen Dan a ƙasar tudu, ba su yarda musu su gangaro zuwa filaye ba.

  2. Su Amoriyawa kuma suka dāge su zauna a Dutsen-Heres, Aiyalon, da Sha’albim. Amma yayinda mutanen Yusuf suka ƙara ƙarfi, sai suka su yin musu aikin gandu.

  3. Iyakar Amoriyawa kuwa daga Mashigin Kunama zuwa Sela da kuma zuwa gaba.

  4. Waɗannan su ne al’umman da Ubangiji ya bari don yă gwada duk waɗannan Isra’ilawan da ba su san yaƙi a Kan’ana ba

  5. (ya yi haka ne domin yă koya wa zuriyar Isra’ilawa waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba),

  6. sarakuna biyar na Filistiyawa, dukan Kan’aniyawa, Sidoniyawa, da kuma Hiwiyawan da suke zaune a duwatsun Lebanon daga Dutsen Ba’al-Hermon zuwa Lebo Hamat.

  7. Isra’ilawa suka zauna tare da Kan’aniyawa da Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa.

  8. Suka auri ’ya’yansu mata, su ma suka bar ’ya’yansu maza suka auri ’ya’yansu mata, suka kuma yi wa gumakansu sujada.

  9. Isra’ilawa suka aikata mugunta a gaban Ubangiji; suka manta da Ubangiji Allahnsu suka kuma bauta wa Ba’al da Ashera.

  10. Fushin Ubangiji kuwa ya yi ƙuna a kan Isra’ila har ya sayar da su ga Kushan-Rishatayim sarkin Aram-Naharayim, a wurinsa ne Isra’ilawa suka zama bayi shekara takwas.

  11. Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa da Yebusiyawan da suka ragu a ƙasar (waɗanda ba Isra’ilawa ba ne),

  12. wato, waɗanda suka ragu a ƙasar, waɗanda Isra’ilawa ba su iya hallakawa ba, su ne Solomon ya ɗauka su zama bayinsa don aikin gandu, kamar yadda yake har wa yau.