Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ambassadors: Ben-Hadad to Ahab

5 ayoyi · 13 fannoni

Ayoyi game da Ben-Hadad to Ahab

  1. Ya aika da ’yan aika zuwa cikin birnin wurin Ahab sarkin Isra’ila yana cewa, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce,

  2. ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne. Mafi kyau cikin matanka da ’ya’yanka nawa ne.’ ”

  3. Sarkin Isra’ila ya amsa, ya ce, “Kamar dai yadda ka faɗa, ranka yă daɗe, sarki. Ni da dukan abin da nake da shi, naka ne.”

  4. Sai ’yan aikan suka sāke dawo suka ce, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce, ‘Na aika ka ba da azurfarka da zinariyarka, matanka da kuma ’ya’yanka.

  5. Amma war haka gobe zan aika shugabannina su bincika fadanka da kuma gidajen shugabanninka. Za su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi.’ ”