Tsallake zuwa abun ciki

Uzziah

33 ayoyi · 4 'yan gida

An kuma san shi da: Azariah, Ozias

Ayoyin da suka ambaci Uzziah

Tace bisa littafi
  1. Wahayi game da Yahuda da Urushalima wanda Ishaya ɗan Amoz ya gani a zamanin da Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, suka yi mulkin Yahuda.

  2. A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali.

  3. Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.

  4. Maganar Ubangiji da ta zo wa Hosiya ɗan Beyeri a zamanin mulkin Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yowash sarkin Isra’ila.

  5. Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila.

  6. Za ku gudu ta wajen kwarin dutsena, gama zai miƙe har zuwa Azel. Za ku gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa a kwanakin Uzziya sarkin Yahuda. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo, tare da duk masu tsarki.

  7. Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yehoram, Yehoram ya haifi Azariya,

  8. Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya,