Tsallake zuwa abun ciki

Leah

32 ayoyi · 10 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Leah

Tace bisa littafi
  1. To, Dina, ’yar da Liyatu ta haifa wa Yaƙub, ta je ta ziyarci matan ƙasar.

  2. ’Ya’yan Liyatu maza, Ruben shi ne ɗan fari na Yaƙub. Sauran su ne, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar da Zebulun.

  3. ’Ya’yan Zilfa maza, mai hidimar Liyatu su ne, Gad da Asher. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaƙub maza, waɗanda aka haifa masa a Faddan Aram.

  4. Waɗannan su ne ’ya’yan Liyatu maza da ta haifa wa Yaƙub a Faddan Aram, ban da ’yarsa Dina. ’Ya’yansa maza da mata duka, mutum talatin da uku ne.

  5. Waɗannan su ne ’ya’yan da Zilfa ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Liyatu. ’Ya’yan duka, su sha shida ne.

  6. A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu.

  7. Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem.