Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Zilpah

9 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Laban kuma ya ba da baranyarsa Zilfa wa ’yarsa tă zama mai hidimarta.

  2. Sa’ad da Liyatu ta ga cewa ta daina haihuwa, sai ta ɗauki mai hidimarta Zilfa ta ba da ita ga Yaƙub tă zama matarsa.

  3. Baranyar Liyatu, Zilfa ta haifa wa Yaƙub ɗa.

  4. Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!” Saboda haka ta ba shi suna Gad.

  5. Zilfa baranyar Liyatu ta haifa wa Yaƙub ɗa na biyu.

  6. Sai Liyatu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Mata za su ce da ni mai farin ciki.” Saboda haka ta sa masa suna Asher.

  7. ’Ya’yan Zilfa maza, mai hidimar Liyatu su ne, Gad da Asher. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaƙub maza, waɗanda aka haifa masa a Faddan Aram.

  8. Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub. Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da ’yan’uwansa, wato, ’ya’yan Bilha maza da kuma ’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da ’yan’uwansa.

  9. Waɗannan su ne ’ya’yan da Zilfa ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Liyatu. ’Ya’yan duka, su sha shida ne.