Skip to content

Johanan

15 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Johanan

  1. Sa’ad da dukan hafsoshin soja tare da mutanensu suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya a matsayin gwamna, sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa. Mutanen da suka zo su ne, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan ɗan Kareya, Serahiya ɗan Tanhumet mutumin Netofa, Ya’azaniya ɗan mutumin Ma’aka, tare da mutanensu.

  2. sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan da Yonatan ’ya’yan Kareya, da Serahiya ɗan Tanhumet maza, ’ya’yan Efai maza, mutumin Netofa, da Yezaniya ɗan mutumin Ma’aka da mutanensu.

  3. Yohanan ɗan Kareya da dukan manyan sojoji da suke a karkara suka zo wurin Gedaliya a Mizfa

  4. Sai Yohanan ɗan Kareya ya yi wa Gedaliya a Mizfa magana a asirce ya ce, “Bari in tafi in kashe Ishmayel ɗan Netaniya, ba kuwa wanda zai sani. Me zai sa ya ɗauke ranka ya watsar da dukan Yahudawan da suka taru kewaye da kai har waɗanda suka ragu na Yahuda su hallaka?”

  5. Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohanan ɗan Kareya, “Kada ka yi irin wannan abu! Abin da kake faɗa game da Ishmayel ba gaskiya ba ne.”

  6. Sa’ad da Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka ji dukan laifofin da Ishmayel ɗan Netaniya ya aikata,

  7. Sa’ad da dukan mutanen da suke tare da Ishmayel suka ga Yohanan ɗan Kareya da shugabannin sojojin da suke tare da shi, sai suka yi farin ciki.

  8. Dukan mutanen da Ishmayel ya kame a Mizfa suka juya, suka tafi wurin Yohanan ɗan Kareya.

  9. Amma Ishmayel ɗan Netaniya da mutanensa takwas suka tsere daga Yohanan suka gudu zuwa wurin Ammonawa.

  10. Sai Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka bi da dukan waɗanda suka tsira daga Mizfa waɗanda ya karɓe daga Ishmayel ɗan Netaniya bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato, sojoji, mata, yara da fadawan da ya kawo daga Gibeyon

  11. Sa’an nan dukan shugabannin sojoji, haɗe da Yohanan ɗan Kareya da Yezaniya ɗan Hoshahiya, da dukan mutane daga ƙarami zuwa babba, suka zo wurin

  12. Saboda haka ya kira Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi da dukan jama’a daga ƙarami zuwa babba.

  13. Azariya ɗan Hoshahiya da Yohanan ɗan Kareya da dukan masu ɗaga kai suka ce wa Irmiya, “Kana ƙarya ne! Ubangiji Allahnmu bai aike ka ka ce, ‘Kada ku tafi Masar don ku zauna a can.’

  14. Saboda haka Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da dukan mutane suka yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da su zauna a ƙasar Yahuda.

  15. A maimako, Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe raguwar Yahuda waɗanda suka dawo su zauna a ƙasar Yahuda daga dukan al’umman inda aka kora su.