Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Seraiah

13 ayoyi · 7 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyatar, su ne firistoci; Serahiya kuma sakatare;

  2. Shewa kuwa magatakarda; Zadok da Abiyatar su ne firistoci;

  3. Elihoref da Ahiya, ’ya’yan Shisha maza, su ne marubuta. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne mai lura da takardu.

  4. Sa’ad da dukan hafsoshin soja tare da mutanensu suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya a matsayin gwamna, sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa. Mutanen da suka zo su ne, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan ɗan Kareya, Serahiya ɗan Tanhumet mutumin Netofa, Ya’azaniya ɗan mutumin Ma’aka, tare da mutanensu.

  5. ’Ya’yan Kenaz maza su ne, Otniyel da Serahiya. ’Ya’yan Otniyel maza su ne, Hatat da Meyonotai.

  6. Meyonotai shi ne mahaifin Ofra. Serahiya shi ne mahaifin Yowab, mahaifin Ge-Harashim. An kira shi haka domin mutanensa masu sana’ar hannu ne.

  7. Akwai Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya. Yoshibiya ɗan Seraya ne. Serahiya kuma ɗan Asiyel ne.

  8. Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci; Shafsha shi ne magatakarda;

  9. da Serahiya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, mai lura da abubuwa a cikin gidan Allah,

  10. A maimakon haka, sai sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, Serahiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel su kama Baruk marubuci da Irmiya annabi. Amma Ubangiji ya ɓoye su.

  11. sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan da Yonatan ’ya’yan Kareya, da Serahiya ɗan Tanhumet maza, ’ya’yan Efai maza, mutumin Netofa, da Yezaniya ɗan mutumin Ma’aka da mutanensu.

  12. Jawabin da annabi Irmiya ya ba Serahiya, ɗan Neriya, wato, jikan Ma’asehiya, lokacin da ya tafi tare da Zedekiya, Sarkin Yahuda, zuwa Babilon a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Serahiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi.

  13. Irmiya kuwa ya ce wa Serahiya, “Lokacin da ka kai Babilon, sai ka karanta dukan maganan nan.