Tsallake zuwa abun ciki

Job

53 ayoyi · 3 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Job

Tace bisa littafi
  1. Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba.

  2. Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi.

  3. Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka.

  4. na saurare ku da kyau. Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi; ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa.

  5. “Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce; ka sa hankali ga kowane abin da zan faɗa.

  6. “Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni; ka yi shiru zan yi magana.

  7. “Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi, amma Allah ya hana mini hakkina.

  8. Wane mutum ne kamar Ayuba, wanda yake shan ba’a kamar ruwa?

  9. ‘Ayuba ya yi magana cikin rashin sani; maganganunsa na marar hikima ne.’

  10. Kash, da za a gwada Ayuba har ƙarshe, domin yana ba da amsa kamar mugun mutum.

  11. Saboda haka Ayuba ya buɗe baki yana magana barkatai; yana ta yawan magana ba tare da sani ba.”

  12. “Ka saurari wannan Ayuba; ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah.

  13. Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce,

  14. Ubangiji ya ce wa Ayuba,

  15. Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji,

  16. Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa,

  17. Sa’an nan Ayuba ya amsa wa Ubangiji,

  18. Bayan Ubangiji ya gaya wa Ayuba waɗannan abubuwa, ya ce wa Elifaz mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokanka guda biyu domin ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.

  19. Saboda haka yanzu sai ku ɗauki bijimai guda bakwai, da raguna bakwai, ku je wurin bawana Ayuba ku miƙa hadaya ta ƙonawa domin kanku. Bawana Ayuba zai yi muku addu’a zan kuwa karɓi addu’arsa in bi da ku nisa da wawancinku. Ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba yadda bawana Ayuba ya yi ba.”

  20. Saboda haka Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa da Zofar mutumin Na’ama, suka yi abin da Ubangiji ya gaya masu; Ubangiji kuma ya karɓi addu’ar Ayuba.

  21. Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu.

  22. Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu.

  23. Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar ’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta ’yan’uwansu maza.

  24. Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu.

  25. Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.