Tsallake zuwa abun ciki

Balak

41 ayoyi · 1 ɗan gida

An kuma san shi da: Balac

Ayoyin da suka ambaci Balak

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka ya tafi ya same Balak tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dattawan Mowab. Balak ya tambaye Bala’am ya ce, “Mene ne Ubangiji ya ce?”

  2. Sai Bala’am ya furta saƙon da aka ba shi ya ce, “Tashi, Balak, ka saurara; ka kasa kunne gare ni, ɗan Ziffor.

  3. Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Kada ka la’anta su, kada kuma ka sa musu albarka!”

  4. Bala’am amsa ya ce, “Ban faɗa maka zan yi kaɗai abin da Ubangiji ya ce ba?”

  5. Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Zo in kai ka wani wuri. Wataƙila zai gamshi Allah, yă bari ka la’anta mini su daga can.”

  6. Balak kuwa ya ɗauki Bala’am zuwa ƙwanƙolin Feyor, wanda yake fuskantar hamada.

  7. Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka kuma shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”

  8. Balak ya yi yadda Bala’am ya ce, ya kuwa miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

  9. Fushin Balak ya ƙuna a kan Bala’am. Ya tafa hannunsa, ya ce masa, “Na kira ka don ka la’anta abokan gābana, amma sai ga shi ka sa musu albarka har sau uku.

  10. Bala’am ya ce wa Balak, “Ban faɗa wa ’yan aikan da ka aiko wurina ba cewa,

  11. ‘Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba, kuma dole in faɗa abin da Ubangiji ya ce ne kawai’?

  12. Sa’an nan Bala’am ya tashi ya koma gidan, Balak kuma ya yi tafiyarsa.

  13. Lokacin da Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab, ya yi shiri yă yaƙi Isra’ila, ya aiki Bala’am ɗan Beyor don yă la’anta ku.

  14. Ka fi Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab ne? Ka taɓa ji ya yi hamayya da Isra’ila ko yă yi yaƙi da su?

  15. Ya ku mutanena, ku tuna abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla da kuma amsar da Bala’am ɗan Beyor ya bayar. Ku tuna da tafiyarku daga Shittim zuwa Gilgal, don ku san ayyukan adalcin Ubangiji.”

  16. Duk da haka, ina da abubuwa kima game da kai. Kana da mutane a can waɗanda suke riƙe da koyarwar Bala’am, wanda ya koya wa Balak yă ja hankalin Isra’ilawa su yi zunubi ta wurin cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci.