Tsallake zuwa abun ciki

Abner

53 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Abner

Tace bisa littafi
  1. To, Shawulu yana da ƙwarƙwarar da ake kira Rizfa, ’yar Aiya. Sai Ish-Boshet ya ce wa Abner, “Don me kake kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?”

  2. Abner ya husata saboda abin da Ish-Boshet ya ce, sai ya ce, “Kana tsammani ni mai cin amana ne? Kana zato ni mai goyon bayan Yahuda ne? Tun farko na nuna aminci ga gidan babanka Shawulu, da ’yan’uwansa, da abokansa! Ban kuwa ba da kai a hannun Dawuda ba. Ga shi yanzu a kan mace za ka ga laifina?

  3. Allah yă yi wa Abner hukunci mai tsanani, in ban goyi bayan Dawuda ya sami abin da Ubangiji ya yi masa alkawari da rantsuwa ba.

  4. Ish-Boshet bai ƙara yin karambanin ce wa Abner kome ba, gama yana tsoronsa.

  5. Sai Abner ya aiki manzanni a madadinsa wurin Dawuda su ce masa, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi yarjejjeniya da ni, zan kuwa taimake ka, in juye dukan Isra’ila zuwa ɓangarenka.”

  6. Amma mijin ya raka ta, yana tafe yana kuka, ya bi ta har Bahurim. Sai Abner ya ce masa, “Koma gida!” Sai ya koma.

  7. Abner ya tattauna da dattawan Isra’ila ya ce, “An daɗe kuna nema ku naɗa Dawuda sarkinku.

  8. Abner kuma ya yi magana da mutane Benyamin da kansa. Sa’an nan ya tafi Hebron yă gaya wa Dawuda ko mene ne Isra’ila da kuma dukan gidan Benyamin suke so su yi.

  9. Sa’ad da Abner wanda yake tare da mutane ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda ya shirya masa liyafa tare da mutanensa.

  10. Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Bari in tafi nan da nan in tattara dukan Isra’ila wa ranka yă daɗe, sarki, saboda su yi alkawari da kai, ka kuma ka yi mulki bisa dukansu yadda ranka yake so.” Saboda haka Dawuda ya sallami Abner, ya kuwa tafi lafiya.

  11. Ba a jima ba sai mutanen Dawuda da Yowab suka dawo daga hari. Suka kawo ganima da yawa tare da su. Abner kuwa ya riga ya bar Dawuda a Hebron, domin Dawuda ya sallame shi, shi kuma ya tafi lafiya.

  12. Sa’ad da Yowab da dukan sojoji suka dawo, aka gaya masa cewa Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya sallame shi, ya kuma tafi lafiya.

  13. Sai Yowab ya je wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka. Don me ka ƙyale shi yă tafi? Ga shi kuwa ya tafi!

  14. Ka san Abner ɗan Ner ya zo ne yă ruɗe ka, yă ga fitarka da shigarka, yă kuma binciki kome da kake yi.”

  15. Yowab ya tashi daga gaban Dawuda ya tafi ya aika manzanni su bi Abner. Suka same shi a rijiyar Sira suka komo da shi, Dawuda kuwa bai sani ba.

  16. To, da Abner ya komo Hebron, Yowab ya ratse da shi zuwa hanyar shigar gari kamar zai gana da shi a kaɗaice. Amma a can ya soki Abner a ciki, ya kashe shi don yă rama mutuwar ɗan’uwansa Asahel.

  17. Daga baya, Dawuda ya ji labarin sai ya ce, “Ni da masarautata har abada ba mu da laifi a gaban Ubangiji game da jinin Abner ɗan Ner.

  18. (Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka kashe Abner don yă kashe ɗan’uwansu Asahel a yaƙin Gibeyon.)

  19. Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya.

  20. Suka binne Abner a Hebron, sarki kuwa ya ɗaga murya ya yi kuka a kabarin Abner.

  21. Sarki ya kuma yi wannan waƙar makoki domin Abner ya ce, “Daidai ne Abner yă mutu, kamar yadda marasa bin doka suke mutuwa?

  22. Saboda haka a ranar dukan mutane da dukan Isra’ila suka gane sarki ba shi da hannu a kisan Abner ɗan Ner.

  23. Sa’ad da Ish-Boshet ya ji labari cewa Abner ya mutu a Hebron, sai ya karaya, sai dukan hankalin Isra’ila ya tashi.

  24. Saboda haka Dawuda ya umarci mutanensa, suka kuwa kashe su. Suka yayyanka hannuwansu da ƙafafunsu, suka kuma rataye jikunansu kusa da tafki a Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-Boshet suka binne a kabarin Abner a Hebron.

  25. “Yanzu fa, kai kanka ka san abin da Yowab ɗan Zeruhiya ya yi mini. Abin da ya yi wa shugabanni biyun nan na mayaƙan Isra’ila, wato, Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya kashe su, ya kuma zub da jininsu a lokacin salama sai ka ce a fage yaƙi, da wannan jini ya yi ɗamara a gindinsa, ya kuma sa takalma a ƙafafunsa.