- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Waƙar Waƙoƙi1
Listen to this chapter
0:00
0:00
Suna da gabatarwar Waƙar
1
Waƙar Waƙoƙin Solomon.
Buririn amarya na kusanci
2
Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa, gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.
3
Ƙanshin turarenka mai daɗi ne; sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne. Shi ya sa mata suke ƙaunarka!
4
Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! Bari sarki yă kai ni gidansa. Ƙawaye Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. Ƙaunatacciya Daidai ne su girmama ka!
Sanin kai da kyau
5
Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa. Ya ku ’yan matan Urushalima, ni baƙa ce kamar tentunan Kedar, kamar labulen tentin Solomon.
6
Kada ku harare ni domin ni baƙa ce, gama rana ta dafa ni na yi baƙa. ’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni suka sa ni aiki a gonakin inabi; na ƙyale gonar inabi na kaina.
Neman ƙaunataccen
7
Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana. Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe kusa da garkunan abokanka?
Shiriya da ƙarfafawa
8
Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba, to, ki dai bi labin da tumaki suke bi ki yi kiwon ’yan awakinki kusa da tentunan makiyaya.
Yabon kyawun amarya
9
Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna.
10
’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau, wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja.
11
Za mu yi ’yan kunnenki na zinariya, da adon azurfa.
Farincikin juna da ƙauna
12
Yayinda sarki yake a teburinsa, turarena ya bazu da ƙanshi.
13
Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni, kwance a tsakanin ƙirjina.
14
Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni daga gonakin inabin En Gedi.
Furucin juna da juna
15
Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki kamar na kurciya ne.
16
Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena! Kai, kana ɗaukan hankali! Gadonmu koriyar ciyawa ce.
Gida da aka gina bisa ƙauna
17
Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu; fir su ne katakan rufin gidanmu.
Use ← → arrow keys to navigate
Settings
Reading Style
Typeface
Font Size px
Reading Width chars
Options
Study Note