Mattiyu 26:59-75
59
Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.
60
Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito. A ƙarshe, biyu suka zo gaba,
61
suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”
62
Sa’an nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”
63
Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai. Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”
64
Sai Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka, nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”
65
Sa’an nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon.
66
Me kuka gani?” Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”
67
Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi
68
suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”
69
To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu mutumin Galili.”
70
Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.”
71
Sa’an nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”
72
Ya sāke mūsu har da rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”
73
Bayan ɗan lokaci, sai na tsattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.”
74
Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!” Nan da take, sai zakara ya yi cara.
75
Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.
Settings