Mattiyu 21:1-18
1
Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu,
2
yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini.
3
In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.”
4
Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa,
5
“Ku ce wa Diyar Sihiyona, ‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki, mai tawali’u yana a kan jaki, a kan aholaki, ɗan jaki.’ ”
6
Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su.
7
Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu.
8
Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya.
9
Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Hosanna a cikin sama!”
10
Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?”
11
Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”
12
Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai.
13
Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”
14
Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su.
15
Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.
16
Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa, “ ‘Daga leɓunan yara da jarirai kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?”
17
Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.
18
Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa.
Settings