Skip to content
Markus 1:14-29

Markus 1:14-29

14
Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah.
15
Yana cewa, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”
16
Yayinda Yesu yake tafiya a gaɓar Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗan’uwansa Andarawus, suna jefa abin kamun kifi a cikin tafkin, domin su masunta ne.
17
Yesu ya ce, “Ku zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.”
18
Nan da nan, suka bar abin kamun kifinsu, suka bi shi.
19
Da ya yi gaba kaɗan, sai ya ga Yaƙub ɗan Zebedi, da ɗan’uwansa Yohanna a cikin jirgin ruwa, suna gyaran abin kamun kifinsu.
20
Ba da ɓata lokaci ba, ya kira su, sai suka bar mahaifinsu Zebedi a cikin jirgin ruwan, tare da ’yan haya, suka kuwa bi shi.
21
Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majami’a ya fara koyarwa.
22
Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba.
23
Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce,
24
“Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!”
25
Yesu ya tsawata masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!”
26
Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu.
27
Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa kuma da iko! Yana ma ba wa mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.”
28
Labari game da shi ya bazu nan da nan ko’ina a dukan yankin Galili.
29
Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options