Skip to content
Yoshuwa 13:1-22

Yoshuwa 13:1-22

1
Sa’ad da Yoshuwa ya tsufa, Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi kuma akwai sauran ƙasa mai fāɗi da ba ku riga kun mallaka ba.
2
“Ga ƙasar da ta rage, “dukan yankunan Filistiyawa da na Geshurawa.
3
Daga Kogin Shihor a gabashin Masar zuwa sashen Ekron a arewa, dukan wannan ƙasa ana lissafta ta a cikin ƙasar Kan’aniyawa, ko da yake tana a sashen da sarakuna biyar na Filistiyawa na Gaza, Ashdod, Ashkeloniyawa, Gat da Ekron; na Awwiyawa.
4
Daga wajen kudu kuma, dukan ƙasar Kan’aniyawa ce. Iyakarta a arewa ta fara daga Ara ta Sidoniyawa har zuwa Afek, ta zarce har zuwa iyakar Amoriyawa;
5
da ƙasar Gebaliyawa; da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba’al-Gad a gindin Dutsen Hermon zuwa Lebo Hamat.
6
“Dukan mazauna kan yankunan tuddai daga Lebanon zuwa Misrefot Mayim, wato, dukan Sidoniyawa, ni da kaina zan kore su a gaban Isra’ilawa. Ka tabbata ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka,
7
ka raba ta tă zama gādo wa kabilu tara da kuma rabin kabilar Manasse.”
8
Rabin kabilar Manasse, mutanen Ruben da mutanen Gad suka karɓi rabonsu na gādo wanda Musa ya ba su a gabashin Urdun. Abin da Musa bawan Ubangiji ya ba su ke nan.
9
Wannan ya tashi daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, ya kuma haɗa da ƙasar da take tudun Medeba har zuwa Dibon,
10
da dukan garuruwan Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon, har zuwa iyakar Ammonawa.
11
Haɗe da Gileyad, inda mutanen Geshur da Ma’aka suke. Dukan Dutsen Hermon, da dukan Bashan har zuwa Saleka,
12
wato, dukan masarautar Og a Bashan, wanda ya yi mulkin Ashtarot da Edireyi, yana cikin waɗanda suke na ƙarshe da ba a kashe ba a cikin Refahiyawa. Musa ya ci su da yaƙi, ya ƙwace ƙasarsu.
13
Amma Isra’ilawa ba su kori mutanen Geshur da Ma’aka ba, saboda haka suka ci gaba da zama cikin Isra’ilawa har wa yau.
14
Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa da ake miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.
15
Ga abin da Musa ya ba kabilar Ruben bisa ga iyalansu.
16
Abin da ya kama daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba
17
zuwa Heshbon, da dukan garuruwan kan tudu, haɗe da Dibon, Bamot Ba’al, Bet-Ba’al-Meyon,
18
Yahza, Kedemot, Mefa’at,
19
Kiriyatayim, Sibma, Zeret Shahar kan tudu cikin kwari,
20
Bet-Feyor, gangaren Fisga da Bet-Yeshimot,
21
dukan garuruwan da suke kan tudu da dukan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Musa ya yi nasara da shi, da shugabannin Midiyawa, wato, Ewi, Rekem, Zur, Hur, da Reba, sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.
22
Ƙari a kan waɗanda aka kashe a yaƙi, Isra’ilawa suka kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi don yana duba.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options