Yohanna 1:26-50
26
Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba.
27
Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.”
28
Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma.
29
Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!
30
Wannan shi ne wanda nake nufi sa’ad da na ce, ‘Mutum mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’
31
Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Isra’ila.”
32
Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa.
33
Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’
34
Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”
35
Kashegari kuma Yohanna yana can tare da biyu daga cikin almajiransa.
36
Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!”
37
Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.
38
Da juyewa, sai Yesu ya ga suna bin sa, sai ya tambaye, su ya ce, “Me kuke nema?” Suka ce, “Rabbi” (wato, “Malam”), “ina kake da zama?”
39
Ya amsa musu ya ce, “Ku zo, za ku kuma gani.” Saboda haka suka je suka ga inda yake da zama, suka kuma zauna a can tare da shi. Wajen sa’a ta goma ce kuwa.
40
Andarawus ɗan’uwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun nan da suka bi Yesu bayan da suka ji maganar Yohanna a kan Yesu.
41
Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗan’uwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi).
42
Ya kuma kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan).
43
Kashegari Yesu ya yanke shawara yă tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, “Bi ni.”
44
Filibus, kamar Andarawus da Bitrus shi ma daga garin Betsaida ne.
45
Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa, Yesu Banazare, ɗan Yusuf.”
46
Natanayel ya ce, “A Nazaret! Wani abin kirki zai iya fito daga can?” Filibus ya ce, “Zo ka gani.”
47
Da Yesu ya ga Natanayel yana zuwa, sai ya yi magana game da shi cewa, “Ga mutumin Isra’ila na gaske wanda ba shi da ha’inci.”
48
Natanayel ya yi tambaya ya ce, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa ya ce, “Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yă kira ka.”
49
Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Isra’ila.”
50
Yesu ya ce, “Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka.”
Settings