Ezekiyel 23:1-32
1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, an yi mata biyu, ’yan matan mahaifiya guda.
3
Suka zama karuwai a Masar, suka yi karuwanci tun daga ƙuruciyarsu. A wancan ƙasar an rungumi mamansu da ƙirjinsu na budurwanci.
4
Sunan babbar Ohola, ƙanuwarta kuwa Oholiba. Sun zama nawa suka kuma haifi ’ya’ya maza da mata. Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.
5
“Ohola ta shiga karuwanci yayinda take zamana; ta kuwa yi ta kai da kawowa da kwartayenta, Assuriyawa, mayaƙa
6
waɗanda suke saye da shunayya, gwamnoni da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha’awa, suna bisa kan dawakai.
7
Ta ba da kanta ga duk waɗanda suke masu ilimin Assuriya ta kuma ƙazantar da kanta da dukan gumaka na kowa da take kai da kawowa a cikinsu.
8
Ba ta bar karuwancin da ta fara a Masar ba, sa’ad da take budurwa maza sun kwana da ita, suka rungumi ƙirjinta suka kuma biya kwaɗayinsu a kanta.
9
“Saboda haka na bashe ta ga kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.
10
Suka tuɓe ta tsirara, suka kwashe ’ya’yanta maza da mata suka kuma kashe ta da takobi. Ta kuwa zama abin karin magana a cikin mata, aka kuma yi mata hukunci.
11
“Ƙanuwarta Oholiba kuwa ta ga wannan, duk da haka cikin kai da kawowarta da karuwancinta ta fi ’yar’uwar lalacewa.
12
Ita ma ta yi ta kai da kawowa cikin Assuriyawa, gwamnoni da manyan sojoji; mayaƙa masu saye da kayan yaƙi, suna bisa dawakai, dukansu samari ne masu bansha’awa.
13
Na ga cewa ita ma ta ƙazantar da kanta; dukansu biyu sun bi hanya guda.
14
“Amma karuwancinta ya zarce. Ta ga an zāna mutane a kan bango, siffofin sojojin Kaldiyawa suna cikin jajjayen riguna,
15
da ɗamara a gindinsu da rawuna a kansu suna kaɗawa falfal; dukansu sun yi kamar jarumawan kekunan yaƙin Babiloniyawa ’yan Kaldiya.
16
Nan da nan da ta gan su, sai ta yi sha’awarsu ta aika da ’yan aika zuwa wurinsu a Kaldiya.
17
Sai Babiloniyawan suka zo wurinta, zuwa gadon soyayya, cikin kai da kawowarsu suka ƙazantar da ita. Bayan sun ƙazantar da ita, sai ta ji ƙyamarsu, ta rabu da su.
18
Sa’ad da ta ci gaba da yin karuwancinta a fili ta kuma nuna tsiraicinta, sai na ji ƙyamarta, na rabu da ita, kamar dai yadda na rabu da ’yar’uwarta.
19
Duk da haka sai ta yi ta ƙara fasikanci tana tuna da kwanakin budurcinta, sa’ad da take karuwa a Masar.
20
A can ta yi ta kai da kawowa da kwartayenta, waɗanda al’auransu kamar na jakuna ne waɗanda maniyyinsu kuwa kamar na dawakai ne.
21
Haka kika yi ta lalacin budurcinki, sa’ad da a Masar aka rungumi ƙirjinta aka tattaɓa nononta.
22
“Saboda haka, Oholiba, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan zuga kwartayenki su yi gāba da ke, su waɗanda kika ji ƙyamarsu, zan kuma kawo su su yi gāba da ke daga kowane gefe,
23
Babiloniyawa da dukan Kaldiyawa, mutanen Fekod da Showa da Kowa, da dukan Assuriyawa, samari masu bansha’awa, dukan gwamnoni da manyan sojoji, hafsoshin keken yaƙin da mutane masu manyan matsayi, dukansu a bisa dawakai.
24
Za su yi gāba da ke da kayan yaƙi, kekunan yaƙi da kekunan doki da mutane masu yawa; za su ja dāgā a kanki a kowane gefe da garkuwoyi manya da ƙanana da kuma hulunan kwano. Zan miƙa ke gare su don hukunci, za su kuma hukunta ki bisa ga shari’arsu.
25
Zan nuna fushin kishina a kanki, za su kuwa wulaƙanta ki da fushi. Za su yanke hancinki da kunnuwanki, waɗanda suka rage miki kuma za a kashe su da takobi. Za su kama ’ya’yanki maza da mata, waɗanda suka rage miki kuwa za a ƙone su da wuta.
26
Za su tuɓe tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau.
27
Ta haka zan tsai da marmari da kuma karuwancin da kika fara a Masar. Ba za ki dubi waɗannan abubuwa da marmari ko ki ƙara tuna da Masar ba.
28
“Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina shirin miƙa ki ga waɗanda suke ƙinki, ga waɗanda kika ji ƙyamarsu kika rabu da su.
29
Za su hukunta ki da ƙiyayya su kuma kwashe kome da kika yi wahalarsa. Za su bar ki tsirara tik, kunyan karuwancinki kuma zai tonu. Marmarinki da fasikancinki
30
sun jawo miki wannan, domin ki yi ta kai da kawowa cikin ƙasashe kina ƙazantar da kanki da gumakansu.
31
Kin bi hanyar ’yar’uwarki; saboda haka zan sa kwaf nata a hannunki.
32
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Za ki sha kwaf na ’yar’uwarki, kwaf wanda yake da girma da kuma zurfi; zai jawo dariya da kuma reni gama yana ɗauke da abubuwa da yawa.
Settings