2 Tarihi 20:15-24
15
Ya ce, “Saurara, Sarki Yehoshafat da dukan waɗanda suke zama a Yahuda da Urushalima! Ga abin da Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku ji tsoro ko ku fid da zuciya saboda wannan babbar runduna. Gama yaƙin ba naku ba ne, amma na Allah.
16
Gobe ku fito ku gangara ku yaƙe su. Za su yi ta haurawa ta Mashigin Ziz, ku kuwa za ku same su a ƙarshen kwari a Hamadan Yeruwel.
17
Ba lalle ba ne ku yi wannan yaƙi. Ku dai, ku ja dāgā, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ba ku, ya Yahuda da Urushalima. Kada ku ji tsoro; kada ku karai. Ku fito don ku fuskance su gobe, Ubangiji kuwa zai kasance tare ku.’ ”
18
Yehoshafat ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada a gaban Ubangiji.
19
Sa’an nan waɗansu Lawiyawa daga Kohatawa da Korayawa suka tashi tsaye suka yabe Ubangiji, Allah na Isra’ila, da babbar murya sosai.
20
Da sassafe suka tashi suka nufi Hamadan Tekowa. Yayinda suka kama hanya, Yehoshafat ya tsaya ya ce, “Ku saurare ni, Yahuda da mutanen Urushalima! Ku amince da Ubangiji Allahnku za a kuwa kafa ku; ku amince da annabawansa za ku kuwa yi nasara.”
21
Bayan suka yi shawara tare da shugabanni, sai ya zaɓi mutanen da za su ja gaban sojoji suna waƙa ga Ubangiji suna yabonsa saboda tsarkinsa suna cewa, “Ku yi godiya ga Ubangiji, gama ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”
22
Da suka fara waƙa, suna kuma yabo, sai Ubangiji ya kai hari a kan mutanen Ammon da Mowab da Dutsen Seyir, waɗanda suka kawo hari a Yahuda, aka kuwa ci su da yaƙi.
23
Mutanen Ammon da Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa’ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka juna.
24
Sa’ad da mutanen Yahuda suka zo wurin da yake fuskantar hamada, suka duba ta wajen babban rundunar, sai suka ga gawawwaki birjik a ƙasa; babu wani wanda ya kuɓuta.
Settings