Skip to content
2 Tarihi 20:31-37

2 Tarihi 20:31-37

31
Ta haka Yehoshafat ya yi mulki a bisa Yahuda. Yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya zama sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa Azuba ce, ’yar Shilhi.
32
Ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa bai kuwa kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji.
33
Duk da haka ba a kawar da masujadai kan tudu ba, domin har yanzu mutanen ba su tsayar da zukatansu ga Allahn kakanninsu ba.
34
Sauran ayyukan mulkin Yehoshafat, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a tarihin Yehu ɗan Hanani, waɗanda aka rubuta a littafin sarakunan Isra’ila.
35
Daga baya, Yehoshafat sarkin Yahuda ya haɗa kai da Ahaziya sarkin Isra’ila, wanda yake da laifin mugunta.
36
Ya yarda da shi su gina jiragen ruwan kasuwanci. Bayan aka gina waɗannan a Eziyon Geber,
37
Eliyezer ɗan Dodabahu na Maresha ya yi annabci a kan Yehoshafat cewa, “Domin ka haɗa kai da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Jiragen ruwan kuwa suka farfashe, ba a kuwa iya sa su je kasuwanci ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options