Skip to content
1 Sama’ila 17:32-51

1 Sama’ila 17:32-51

32
Da Shawulu ya tambayi Dawuda, sai Dawuda ya ce masa, “Kada kowa yă damu saboda wannan Bafilistin. Bawanka zai je yă yi faɗa da shi.”
33
Shawulu ya ce, “Ba za ka iya yin faɗa da wannan Bafilistin ba, ya daɗe yana yaƙi, ya yi yaƙi tun yana saurayi. Ga shi kuwa kai ɗan yaro ne kawai.”
34
Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita.
35
Nakan bi ta a baya in buga ta in kuma ƙwato tunkiyar daga bakinta. In kuma ta taso mini, nakan cafke ta a gashinta in buga ta in kashe.
36
Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai.
37
Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai.”
38
Sai Shawulu ya kawo kayan yaƙinsa ya sa wa Dawuda. Ya sa masa hular kwanon da aka yi da tagulla a kansa, ya kuma sa masa rigar ƙarfensa.
39
Dawuda ya ɗaura māshin Shawulu a sulken, ya yi ƙoƙari yă zaga, sai ya ji ba zai iya ba saboda bai saba ba. Ya cewa Shawulu, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, domin ban saba ba.” Don haka ya tuɓe su.
40
Sai ya ɗauki sandansa, ya zaɓi duwatsu guda biyar masu sulɓi daga cikin rafi, ya sa su a ’yar jakarsa ta makiyaya; ya kuma ɗauki majajjawarsa, ya tafi, yă fuskanci Bafilistin.
41
Ana ciki haka, sai Bafilistin nan shi ma ya fita yana gusowa zuwa wurin Dawuda. Mai riƙe masa garkuwar yaƙi kuwa yana tafe a gabansa.
42
Bafilistin ya dubi Dawuda daga sama har ƙasa, ya gan dai ɗan yaro ne kawai, kyakkyawa kuma mai ƙoshin lafiya, sai ya rena shi.
43
Ya ce masa, “Kana tsammani ni kare ne da za ka zo mini da sanda?” Sai ya la’anci Dawuda da sunayen allolin Filistiyawa.
44
Ya ce, “Zo nan, ni kuwa zan ba da naman jikinka ga tsuntsayen sama da namun jeji su ci.”
45
Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.
46
Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila.
47
Duk waɗanda suka taru a nan za su san cewa ba da māshi ko takobi ne Ubangiji yake ceto ba, gama yaƙin nan na Ubangiji ne, shi kuwa zai bashe ku duka a hannuwanmu.”
48
Yayinda Bafilistin yana matsowa kusa domin yă fāɗa wa Dawuda, sai Dawuda ya ruga a guje zuwa bakin dāgā don yă same shi.
49
Ya sa hannu a jakarsa ya ɗauki dutse, ya sa cikin majajjawa ya wurga, dutsen kuwa ya bugi Bafilistin a goshi, dutsen ya shiga cikin goshinsa, sai Bafilistin ya fāɗi rubda ciki.
50
Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara a kan Bafilistin. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.
51
Dawuda ya ruga ya tsaya a bisan Bafilistin, ya zare takobin Bafilistin daga kubensa, ya datse masa kai da shi. Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka juya suka gudu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options