Skip to content
1 Sama’ila 17:12-30

1 Sama’ila 17:12-30

12
To, Dawuda dai ɗan wani mutumin Efratawa ne mai suna Yesse, shi mutumin Betlehem ne a cikin Yahudiya. Yesse yana da yara maza takwas, a zamanin Shawulu kuwa, Yesse ya riga ya tsufa.
13
Manyan ’ya’yansa maza uku, sun bi Shawulu wajen yaƙi. Ɗansa na fari shi ne Eliyab, na biyu shi ne Abinadab, na uku kuwa shi ne Shamma.
14
Dawuda shi ne ɗan autansu. Manyan ’yan mazan nan uku suka bi Shawulu.
15
Amma Dawuda yakan tafi sansanin Shawulu lokaci-lokaci yă kuma koma Betlehem don yă yi kiwon tumakin mahaifinsa.
16
Kwana arba’in cif, Bafilistin nan ya yi ta fitowa kowane safe da kuma kowace yamma.
17
Yesse ya ce wa ɗansa Dawuda, “Ka ɗauki wannan gasasshen hatsi da waɗannan curin burodi goma, ka kai wa ’yan’uwanka a sansani da sauri.
18
Ka haɗa da waɗannan cuku guda goma, ka kai wa komandan rundunarsu. Ka ga lafiyar ’yan’uwanka, ka kawo mini labari daga wurinsu.
19
Suna tare da Shawulu da kuma dukan mutanen Isra’ila a Kwarin Ela, suna can suna yaƙi da Filistiyawa.”
20
Kashegari da sassafe, Dawuda ya tashi ya bar tumakinsa wa wani yă lura da su, sai ya ɗauki kayansa, ya kama hanya kamar yadda Yesse ya umarce shi. Ya isa sansanin daidai sa’ad da rundunar tana fitowa zuwa bakin dāgā, suna kirarin yaƙi.
21
Isra’ila da Filistiyawa suka ja dāgā suna fuskantar junansu.
22
Dawuda ya bar kayansa a wajen wani mai lura da kaya, sai ya ruga zuwa bakin dāgā yă gai da ’yan’uwansa.
23
Da yana magana da su sai Goliyat, jarumin nan Bafilistin daga Gat ya fito daga rundunar Filistiyawa, ya tā da murya kamar yadda ya saba. Dawuda kuwa ya ji shi.
24
Da Isra’ilawa suka ga mutumin, sai dukansu suka gudu saboda tsananin tsoro.
25
Isra’ilawa suka yi ta cewa, “Kun ga yadda wannan mutum yana ta fitowa? Yana fitowa ne don yă kalubalanci Isra’ila. Sarki zai sāka wa mutumin da ya kashe wannan da dukiya mai yawa. Zai kuma ba shi ’yarsa yă aura, yă cire suna mahaifinsa daga biyan kuɗin haraji cikin Isra’ila.”
26
Dawuda ya tambayi mutanen da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilistin nan, ya kuma cire wannan kunya daga Isra’ila? Wane ne wannan bafilistin marar kaciya da yake kalubalantar rundunar yaƙi na Allah mai rai?”
27
Sai suka sāke gaya masa abin da suka faɗa cewa, “Ga abin da zai faru da wanda ya kashe shi.”
28
Da wansa Eliyab, ya ji yana magana da mutanen, sai ransa ya ɓace ƙwarai saboda fushi, sai ya ce wa Dawuda, “Me ka zo yi a nan? Wa kuma ka bar wa ’yan tumakin a jeji? Na san ka da taurinkai, da kuma mugun hali. Ka zo nan ne don ka yi kallon yaƙi kawai.”
29
Dawuda ya ce, “To, yanzu me na yi? Ba zan ma yi magana ba?”
30
Sai ya juya wajen wani kuma ya sāke kawo zancen, mutanen kuwa suka amsa masa kamar dā.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options