Skip to content
1 Sarakuna 22:3-29

1 Sarakuna 22:3-29

3
Sarkin Isra’ila ya ce wa shugabanninsa, “Ba ku san cewa Ramot Gileyad namu ne ba, duk da haka ba mu yi kome ba don mu sāke karɓanta daga sarkin Aram?”
4
Saboda haka ya tambayi Yehoshafat, ya ce, “Za ka tafi tare da ni don in yi yaƙi da Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa wa sarkin Isra’ila, ya ce, “Ni ma kamar ka ne, mutanena kuwa kamar mutanenka, dawakaina kamar dawakanka.”
5
Amma Yehoshafat ya ce wa sarkin Isra’ila, “Da farko mu nemi nufin Ubangiji.”
6
Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa, kamar ɗari huɗu, ya tambaye su, “In kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada in kai?” Suka amsa, “Ka tafi, gama Ubangiji zai ba ka ita a hannunka.”
7
Amma Yehoshafat ya yi tambaya, ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu tambaya?”
8
Sarkin Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, ya ce, “Akwai mutum guda har yanzu wanda ta wurinsa za mu iya nemi nufin Ubangiji, amma na ƙi jininsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai dai mummuna kullum. Shi ne Mikahiya ɗan Imla.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya ce haka.”
9
Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin shugabanninsa ya ce, “Kawo Mikahiya ɗan Imla nan take.”
10
Saye da rigunansu na sarauta, sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zama a kujerun sarautarsu a masussuka ta mashigin ƙofar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu.
11
Zedekiya ɗan Kena’ana kuwa ya yi ƙahonin ƙarfe ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka tunkuyi Arameyawa har su hallaka.’ ”
12
Dukan sauran annabawan suka yi annabci iri abu ɗaya. Suka ce, “Ka yaƙi Ramot Gileyad, ka kuma yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita cikin hannun sarki.”
13
Ɗan aikan da ya je yă kawo Mikahiya, ya ce masa, “Duba, sauran annabawa suna maganar nasara wa sarki, sai ka ce mutum guda. Bari maganarka tă yarda da tasu, ka kuma yi maganar alheri.”
14
Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji mai rai, zan faɗa masa kawai abin da Ubangiji ya faɗa mini.”
15
Da suka kai, sai sarki ya tambaye shi, ya ce, “Mikahiya, mu kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada mu kai?” Ya amsa ya ce, “Yaƙe ta, za ka kuwa yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita cikin hannun sarki.”
16
Sai sarki ya ce masa, “Sau nawa ne zan sa ka rantse cewa ba za ka faɗa mini kome ba sai dai gaskiya a cikin sunan Ubangiji?”
17
Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, kuma Ubangiji ya ce, ‘Waɗannan mutane ba su da maigida. Bari kowa yă tafi gida cikin salama.’ ”
18
Sai sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka cewa bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni, sai mummuna kawai ba?”
19
Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka ka ji maganar Ubangiji. I, na ga Ubangiji zaune a kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye kewaye da shi a dama da hagunsa.
20
Kuma Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab zuwa yaƙi da Ramot Gileyad, yă kuma kai shi mutuwarsa a can?’ “Wani ya ce wannan, wani ya ce wancan.
21
A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’
22
“Ubangiji ya yi tambaya ‘Ta wace hanya?’ Ya ce, “ ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’
23
“Saboda haka yanzu Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawanka. Ubangiji ya zartar maka da masifa.”
24
Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya hau ya mari Mikahiya a fuska. Ya yi tambaya, “A wace hanya ce ruhu daga Ubangiji ya bar ni ya yi maka magana?”
25
Mikahiya ya amsa, “Za ka gane a ranar da ka je ka ɓuya a ciki cikin ɗaki.”
26
Sa’an nan sarkin Isra’ila ya umarta, “Ku kama Mikahiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki.
27
Ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku sa wannan mutum a kurkuku, kuma kada ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa, sai na dawo lafiya.’ ”
28
Mikahiya ya furta, “Idan har ka dawo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana ta wurina ba.” Ya kuma ƙara da cewa, “Ku lura da maganata, dukanku mutane!”
29
Sai sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options