1 Sarakuna 22:5-12
5
Amma Yehoshafat ya ce wa sarkin Isra’ila, “Da farko mu nemi nufin Ubangiji.”
6
Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa, kamar ɗari huɗu, ya tambaye su, “In kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada in kai?” Suka amsa, “Ka tafi, gama Ubangiji zai ba ka ita a hannunka.”
7
Amma Yehoshafat ya yi tambaya, ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu tambaya?”
8
Sarkin Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, ya ce, “Akwai mutum guda har yanzu wanda ta wurinsa za mu iya nemi nufin Ubangiji, amma na ƙi jininsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai dai mummuna kullum. Shi ne Mikahiya ɗan Imla.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya ce haka.”
9
Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin shugabanninsa ya ce, “Kawo Mikahiya ɗan Imla nan take.”
10
Saye da rigunansu na sarauta, sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zama a kujerun sarautarsu a masussuka ta mashigin ƙofar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu.
11
Zedekiya ɗan Kena’ana kuwa ya yi ƙahonin ƙarfe ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka tunkuyi Arameyawa har su hallaka.’ ”
12
Dukan sauran annabawan suka yi annabci iri abu ɗaya. Suka ce, “Ka yaƙi Ramot Gileyad, ka kuma yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita cikin hannun sarki.”
Settings