1 Tarihi 4:24-43
24
Zuriyar Simeyon su ne, Nemuwel, Yamin, Yarib, Zera da Shawulu;
25
Shawulu ya haifi Shallum, Shallum ya haifi Mibsam. Mibsam ya haifi Mishma.
26
Zuriyar Mishma su ne, Hammuwel ɗansa, wanda ya haifi Zakkur, shi Zakkur kuma ya haifi Shimeyi.
27
Shimeyi yana da ’ya’ya maza goma sha shida da ’ya’ya mata shida, amma ’yan’uwansa ba su da ’ya’ya da yawa; saboda haka gidansu gaba ɗaya ba tă zama mai mutane da yawa kamar mutanen Yahuda ba.
28
Sun zauna a Beyersheba, Molada, Hazar Shuwal,
29
Bilha, Ezem, Tolad
30
Betuwel, Horma, Ziklag,
31
Bet-Markabot, Hazar-Susim, Bet-Biri da Sha’arayim. Waɗannan su ne garuruwansu har lokacin mulkin Dawuda.
32
Ƙauyukan da suke kewayensu su ne Etam, Ayin, Rimmon, Token da Ashan, garuruwa biyar;
33
da kuma dukan ƙauyuka kewaye da waɗannan garuruwa har zuwa Ba’al. Waɗannan ne wuraren zamansu. Suka kuma ajiye tarihin zuriya.
34
Zuriyar Simeyon ta ƙunshi Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya.
35
Akwai Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya. Yoshibiya ɗan Seraya ne. Serahiya kuma ɗan Asiyel ne.
36
Akwai Eliyohenai da Ya’akoba, da Yeshohahiya, da Asahiya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benahiya.
37
Akwai Ziza ɗan Shifi. Shifi ɗan Allon ne. Allon ɗan Yedahiya ne. Yedahiya ɗan Shimri ne. Shimri kuma ɗan Shemahiya ne.
38
Mutanen da aka jera sunayensu a bisa, shugabannin gidajensu ne. Iyalansu sun ƙaru sosai,
39
suka tafi bayan garin Gedor wajajen gabashin kwari suna neman makiyaya domin garkunansu.
40
Suka sami makiyaya mai ciyawa mai kyau, ƙasar kuma tana da fāɗi, da salama, kuma zaman lafiya. A dā waɗansu mutanen Ham sun zauna a can.
41
Mutanen da aka jera sunayensu sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda. Suka yaƙi mutanen Ham a wuraren zamansu, haka kuma suka yi da Meyunawa da suke can, suka hallaka su ƙaƙaf, yadda yake har yă zuwa yau. Sa’an nan suka zauna a wurin, gama akwai makiyaya domin garkunansu.
42
Mutum ɗari biyar na waɗannan mutane Simeyon, waɗanda Felatiya, Neyariya, Refahiya da Uzziyel, ’ya’yan Ishi maza suka jagorance, sun mamaye ƙasar tudu ta Seyir.
43
Suka karkashe raguwar Amalekawan da suka tsere, suka kuma zauna a can har yă zuwa yau.
Settings