Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Canaanites: To try Israel
Ayoyi game da To try Israel
Waɗannan su ne al’umman da Ubangiji ya bari don yă gwada duk waɗannan Isra’ilawan da ba su san yaƙi a Kan’ana ba
(ya yi haka ne domin yă koya wa zuriyar Isra’ilawa waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba),
sarakuna biyar na Filistiyawa, dukan Kan’aniyawa, Sidoniyawa, da kuma Hiwiyawan da suke zaune a duwatsun Lebanon daga Dutsen Ba’al-Hermon zuwa Lebo Hamat.
An bar su domin su gwada Isra’ilawa a ga ko za su yi biyayya da umarnin Ubangiji, wanda ya ba wa kakanninsu ta wurin Musa.