Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Siloam

14 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Shallum ɗan Kol-Hoze mai mulkin Mizfa ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Maɓuɓɓuga. Ya sāke gina ta, ya yi mata jinƙa yana sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. Ya kuma gyara katangar tafkin Silowam, ta Lambun Sarki, har zuwa matakalan da suka gangara daga Birnin Dawuda.

  2. “Domin wannan jama’a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa suka yi ta farin ciki a kan Rezin ɗan Remaliya,

  3. Ko kuwa kuna tsammani, sha takwas ɗin nan da suka mutu lokacin da hasumiya a Silowam ya fāɗi a kansu, sun fi dukan sauran mutanen Urushalima laifi ne?

  4. Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho.

  5. Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?”

  6. Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa.

  7. Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki.

  8. Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.”

  9. Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin.

  10. Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.

  11. Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Kai, ba wannan mutum ne ya saba zama yana bara ba?”

  12. Waɗansu suka ce shi mana. Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ya dai yi kama da shi.” Amma shi ɗin ya ce, “Ƙwarai kuwa ni ne.”

  13. Sai suka ce, “To, yaya aka yi idanunka suka buɗe?”

  14. Ya amsa ya ce, “Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari.”