Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sea

23 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance.

  2. Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.

  3. ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.

  4. “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.

  5. Ya tattara ruwan teku cikin tuluna; ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.

  6. Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

  7. Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari.

  8. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.

  9. Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata ku yi rawar jiki a gabana ba? Na sa yashi ya zama iyakar teku, madawwamiyar iyakar da ba zai tsallake ba. Raƙuman ruwa za su iya yin hauka, amma ba za su iya haye ta ba; za su iya yin ruri, amma ba za su iya ƙetare ta ba.

  10. Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.

  11. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

  12. Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

  13. Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.

  14. Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.”

  15. Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”

  16. Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji in kai ne ka ce mini in zo wurinka a kan ruwan.”

  17. Ya ce, “Zo.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu.

  18. Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”

  19. Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”

  20. Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa.

  21. Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?”

  22. Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, “Shiru! Ku natsu!” Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.

  23. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata.