Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sea: Calmed by Jesus

6 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Calmed by Jesus

  1. Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.

  2. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

  3. Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

  4. Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa.

  5. Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?”

  6. Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, “Shiru! Ku natsu!” Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.