Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Proclamation

30 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

  2. Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.”

  3. Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

  4. Daga sarki Nebukadnezzar. Zuwa ga mutane da al’ummai da kuma kowane yare, da suke zama a duniya. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku!

  5. Sai Belshazar ya umarta, aka sa wa Daniyel riga mai shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.