Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prayerfulness

20 ayoyi

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Busa. Ta Dawuda. Ka saurare kalmomina, ya Ubangiji, ka ji ajiyar zuciyata.

  2. Ka saurare kukata na neman taimako, Sarkina da Allahna, gama gare ka nake addu’a.

  3. Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata; da safe na gabatar da bukatuna a gabanka in kuma jira da sa zuciya.

  4. Da rana Ubangiji yakan nuna ƙaunarsa, da dare waƙarsa tana tare da ni, addu’a ga Allah na raina.

  5. A maimakon ƙauna sun sāka mini da zargi, amma ni mutum ne mai addu’a.

  6. Domin ya juye kunnensa gare ni, zan kira gare shi muddin ina da rai.

  7. To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.

  8. ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.

  9. mu kuwa mu mai da halinmu ga yin addu’a da kuma hidimar maganar Allah.”

  10. Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma addu’a ga Allah ba fasawa.

  11. Wajen tsakar rana kashegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yă yi addu’a.

  12. Allah, wanda nake bauta wa da dukan zuciyata cikin wa’azin bisharar Ɗansa, shi ne shaidata a kan yadda kullum ina tunawa da ku

  13. Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.

  14. Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah,

  15. ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina.

  16. Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka.

  17. Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.

  18. ku ci gaba da yin addu’a;

  19. Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako.

  20. Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina.