Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pitcher

12 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. In kana tsoron fāɗa musu, sai ka tafi da bawanka Fura

  2. ka kuma saurari abin da suke faɗi. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali ka auka musu.” Saboda haka sai ya tafi tare da Fura bawansa zuwa sansanin.

  3. Midiyawa, Amalekawa da dukan sauran mutane gabashi suka yi sansani a kwari, kamar fāra. Raƙumansu kuma kamar yashi a bakin teku don sun wuce ƙirge.

  4. Gideyon ya iso daidai wani yana faɗa wa wani aboki mafarkinsa, yana cewa, “Na yi mafarki, na ga dunƙule burodin sha’ir ya fāɗo a tsakiyar sansanin Midiyawa. Ya bugi tentin da ƙarfin da ya sa tenti ta kife a ƙasa.”

  5. Abokinsa ya ce, “Ai wannan ba wani abu ba ne fiye da takobin Gideyon ɗan Yowash, mutumin Isra’ila. Allah ya ba da Midiyawa da dukan sansani a hannuwansa.”

  6. Da Gideyon ya ji mafarkin da fassararsa, sai ya yi wa Allah sujada. Ya koma sansanin Isra’ila ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku tashi! Ubangiji ya ba da sansanin Midiyawa a hannuwanku.”

  7. Ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho da tulu da acibalbal a ciki.

  8. Ya ce musu, “Ku dube ni, ku bi abin da na yi. Sa’ad da na kai sansanin, ku yi daidai abin da na yi.

  9. Sa’ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoninmu, to, ko’ina a kewayen sansanin sai ku busa naku ku kuma yi ihu, ku ce, ‘Don Ubangiji da kuma domin Gideyon.’ ”

  10. Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu.

  11. Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka ɗauki acibalbal a hannuwansu na hagu da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama, sai suka yi ihu, “Takobi don Ubangiji da kuma don Gideyon!”

  12. Dubi samarin Sihiyona masu daraja, waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya, yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa, aikin maginin tukwane!