Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Morning: Offered a part of the daily sacrifice in

6 ayoyi · 27 fannoni

Ayoyi game da Offered a part of the daily sacrifice in

  1. “Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana. ’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya.

  2. Ka miƙa ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma.

  3. A miƙa rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma,

  4. tare da hadaya ta lallausan gari kashi ɗaya bisa goma na efan, kwaɓaɓɓe da kwalaba ɗaya na man zaitun mafi kyau.

  5. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  6. Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki.