Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Modern Samaria: Ready to hear and embrace the gospel

7 ayoyi · 23 fannoni

Ayoyi game da Ready to hear and embrace the gospel

  1. Samariyawa da yawa daga wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”

  2. To, da Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roƙe shi yă zauna da su, ya kuwa zauna kwana biyu.

  3. Saboda kalmominsa kuwa da yawa suka gaskata.

  4. Sai suka ce wa macen, “Yanzu kam mun gaskata, ba don abin da kika faɗa kawai ba; yanzu mun ji da kanmu, mun kuwa san cewa wannan mutum tabbatacce shi ne Mai Ceton duniya.”

  5. Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa.

  6. Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa.

  7. Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.