Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Marriage: Parables from

10 ayoyi · 83 fannoni

Ayoyi game da Parables from

  1. “A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango.

  2. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima.

  3. Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba.

  4. Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu.

  5. Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.

  6. “Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’

  7. “Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu.

  8. Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’

  9. “Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’

  10. “Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.