Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jubilee

56 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “ ‘Ku ƙirga asabbatai bakwai na shekaru bakwai, sau bakwai. Gama asabbatai bakwai na shekaru bakwai za su yi daidai da shekaru arba’in da tara.

  2. Sa’an nan a busa ƙaho a ko’ina, a rana ta goma ga wata na bakwai; a Ranar Kafara, a busa ƙaho a dukan ƙasarku.

  3. Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar ’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa.

  4. Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba.

  5. Gama shekara ce ta murna, za tă kuma zama mai tsarki a gare ku, ku dai ci abin da aka ɗauka kai tsaye daga gonaki.

  6. “ ‘A wannan Shekara ta Murna, kowa zai koma ga mallakarsa.

  7. “ ‘In ka sayar da gona wa wani daga mutanen ƙasarka, ko ka saya wata gona daga gare shi, kada ku cuci juna.

  8. Sa’ad da mutum ya sayi fili daga abokin zamansa, kuɗin zai kasance bisa ga yawan shekara hamsin ta murna da suka wuce, da kuma bisa ga yawan shekarun noma da suka rage kafin wata shekara hamsin ta murna.

  9. Idan shekarun suna da yawa, sai ku kara kuɗin filin, idan kuma shekarun ba su da yawa, sai ku rage kuɗin filin, gama ainihin abin da ake sayar maka shi ne yawan hatsin.

  10. Kada ku cuci juna, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  11. “ ‘Ku bi farillaina, ku kuma yi hankali ga kiyaye dokokina, za ku kuwa zauna lafiya a ƙasar.

  12. Sa’an nan ƙasar za tă ba da amfaninta, za ku kuwa ci ku ƙoshi, ku kuma zauna lafiya.

  13. Mai yiwuwa ku ce, “Me za mu ci a shekara ta bakwai in ba mu yi shuki ko girbin hatsinmu ba?”

  14. Zan aika muku da irin albarka a shekara ta shida har da ƙasar za tă ba da amfani isashe na shekara uku.

  15. Yayinda kuke shuki a shekara ta takwas, za ku kasance da raguwa hatsi na shekarar da ta wuce, za ku kuma ci gaba da ci daga gare shi har girbin shekara ta tara yă shigo.

  16. “ ‘Kada a sayar da gona ɗinɗinɗin, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi ne kawai, kuma ’yan haya nawa.

  17. Ko’ina a ƙasar da kuke da mallaka, dole ku tanadar da dama fansar ƙasar.

  18. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar.

  19. In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta,

  20. sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  21. Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  22. “ ‘In mutum ya sayar da gida a birni mai katanga, yana da izini yă fanshe shi a ƙarshen shekara guda, bayan ya sayar da shi.

  23. In ba a fanshe shi a ƙarshen shekara ba, gidan da yake a birni mai katanga, zai zama mallakar na ɗinɗinɗin na mai sayan da kuma zuriyarsa. Ba za a mai da shi a Shekara ta Murna ba.

  24. Amma za a ɗauki gidaje a ƙauyuka marasa katanga kewaye da su daidai da gonaki. Za a iya fanshe su, a kuma mayar da su a Shekara ta Murna.

  25. “ ‘Kullum, Lawiyawa suna da izini su fanshi gidajensu a biranen Lawiyawa waɗanda suka mallaka.